Pulse.ng logo
Go

Wata sabuwa Ɗan ɗan Atiku Abubakar da tsohon matar sa sun sa zare game da wa zai kula da diyar su

Bayan rigimar da Aminu yayi ita dai Bolori ta jajirce wajen hana shi ɗaukan Amira.

  • Published:

Daya daga cikin yaran tsohon mataimakin shugaban kasa mai suna Aminu tare da tsohon matar sa Bolori sun dama a safiyar ranar alhamis game da wa zai kula da rainon ɗiyar su Amira.

A bisa labarin da Lindaikejiblog ya fitar, Bolori ta dira makarantar ɗiyar dake  parkview estate nan jihar Legas tare da takarda da kotu ya bata na damar kula da diyar wanda ke hannun shi Aminu tunda suka rabu.

Da jin haka Aminu yayi tafiyar iska zuwa makarantar tare da tawagar jami’an tsaron sa domin hana ta daukan ɗiyar.

Bayan rigimar da Aminu yayi ita dai Bolori ta jajirce wajen hana shi daukan Amira.

Bolori ta jajirce wajen hana shi dauka diyar su (Lindaikejisblog) play

Bolori ta jajirce wajen hana shi dauka diyar su (Lindaikejisblog)

 

Jim kadan bayan jayayya da tada jijiyoyi da suka yi jami’an hukumar yan sanda suka shiga tsakanin su har suka tafi dasu karamar hedkwatar su dake nan Ikoyi.

Zasu gana da kwamishnan yan sanda na jihar Imohimi Edgal domin ya sulhunta su.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.