Advertisement

Gaskiyar lamari game da hotunan Maryam Booth da Sadiq Zazzabi

___9153560___2018___11___30___12___mlmibrahimsharukhan_46790736_529785924114783_4293451232860115586_n
___9153560___2018___11___30___12___mlmibrahimsharukhan_46790736_529785924114783_4293451232860115586_n
Jaruman a cikin sabbin hotunan da suka yi tare sun jawo hankalin jama'a inda da yawa ana hasashe cewa akwai wani alakar soyayya dake tsakanin su.
Advertisement

Fitacciyar jarumar Kannywood Maryam Booth da shahararren mawaki Sadiq Zazzabi sun mamaye kafafen sada zumunta bisa ga dalilin hotunan da suka dauka.

Advertisement

Jaruman a cikin sabbin hotunan da suka yi tare sun jawo hankalin jama'a inda da yawa ana hasashe cewa akwai wani alakar soyayya dake tsakanin su kuma hotunan na kafin auren su ne.

___9153562___2018___11___30___12___mlmibrahimsharukhan_46544082_191380598476217_3540165140702877731_n

Masoyan jaruman da masu bibiyan labarun dandalin fina-finan hausa suna ta masu fatan alheri da zaton cewa suna shirin bikin auren su.

Sai dai alamu sun nuna cewa hasashen da jama'a keyi game da hotunan ba gaskiya bane.

Advertisement
___9153561___2018___11___30___12___mlmibrahimsharukhan_45273962_789036171439985_2313109332601363770_n

Shafin Kannywoodexclusive ta bayyana cewa jaruman sun dauki hotunan ne domin shirya ma wata sabuwar shiri da shahararren mai gabatar da biki Mc Ibrahim Sharukhan ke shiryawa mai taken "gidan biki".

Shima Mc Ibrahim ya gasgata hakan inda ya wallafa hotunan jaruman a shafin sa na instagram tare da rubuta "Allah ya kaimu gidan biki".

Kamar yadda masu karatu zasu gani, hotunan dai sun birge kuma shahararren mai hoto Umar Balancy ya dauki hotunan wanda da hakan jama'a ke ganin cewa lamarin gaskiya ne.

Advertisement
Advertisement
Latest Videos
Advertisement