Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya rantsar da sabbin Sanatoci Ahmed Baba-Kaita da Lawal Gumau shigar su farfajiyar majalisar.

An rantsar dasu a zaman da majalisar tayi ranar 10 ga watan Oktoba.

Sanatocin sunyi nasarar lashe zaben cike gurbi da aka gudanar a jihar Bauchi da Katsina.

Ahmed Babba-Kaita yayi nasarar lashe zaben cike gurbin da aka gudanar a watan Agusta na wakiltar arewacin jihar Katsina karkashin jam'iya mai mulki ta APC.

Ya doke dan uwan shi na jam'iyar PDP a zaben domin maye gurbin marigayi Bukar Mustapha a majalisar dokokin tarayya.

Shima Lawal Gumau yayi nasarar lashe zaben jihar Bauchi wanda aka gudanar ranar 11 ga watan Agusta karkashin jam'iyar APC.

Zai wakilci yankin kudancin jihar Bauchi a zauren majalisar dattawa bayan yayi nasarar maye gurbin marigayi Ali Wakili wanda ya rasu cikin watan Maris na 2019.