Majalisar dokoki na jihar Sokoto ta tabbatar da Alhaji Mannir Dan Iya A matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar.

An tabbatar da hakan ne sakamakon kudurin da mataimakin shugaban jam'iya mafi rinjaye, Alhaji Ibrahim Sarki ya shigar bayan da gwamna Aminu Tambuwal ya tura sunan Dan iya domin a tantance.

Bayan muhawara da aka yi kan kudurin, kakakin majalisar Alhaji Salihu Maidaji ya tabbatar da matsayin sabon mataimakin gwamna.

Mannir Dan-Iya zai maye gurbin tsohon mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Ahmed Aliyu, wanda ya sauka daga mukamin a ranar 13 ga watan Nuwamba.

Tsohon mataimakin gwamnan ya sauka ne daga matsayin bayan da ya samu takardar tsayawa takarar gwamna  na jam'iyar APC a zabe dake gabatowa.