Kungiyar tare da gamayyar ma'aitakan ma'aikatar ilimi na jihar zasu hada kai wajen samar ma dan takarar jam'iyar PDP kuri'u a zaben shugaban kasa.

Malaman sun bayyana matakin da suka dauka yayin da suka gana da mataimakin shugaban cibiyar yakin neman zaben Atiku kuma tsohon gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel.

Gbenga Daniel
Gbenga Daniel

Sun bayyana cewa " Babu tsari a tarayya kai ga jihohi dangane da harkar ilimi."

Malaman sunce yan siyaya sun talautar da jama'a kai ga har suna iya shawo kansu da kudi wajen zabe wanda ke haifar da samun shugabanni.

Kungiyar ta jinjina ma anniyar Atiku wajen samad da ayyukan yi ga dinbim jama'a dake kasar. Tace matakin zata daukaka Najeriya bisa tafarkin cigaba.

Daya daga cikin malaman yana mai cewa " A shirye malamai suke wajen mara ma dan takarar PDP baya domin hana faruwar kwatancin abun da ya faru a 2015. Muna tare da Atiku kuma duk abun da zamu yi zamu yishi ne yadda ya kamata."

A jawabin sa, Gbenga Daniel ya tabbatar ma malaman burin Atiku wajen sauya fasalin kasa.

Daniel yace " Babban kalubale da ya kamata mu fuskanta shine tashi tsaye wajen nuna rashin amincewa da gwamnati dake saman gado."

Ya kara da cewa ganawar da malaman yana da muhimmanci domin " cinma manufa a zaben dake gabatowa."

Yace " Buhari ya gaza samun nasara a matakai da ya dauka na bunkasa tattalin arzikin da kuma harkar tsaro da cin hanci." 

Tsohon gwamnan ya kara da cewa za zaben bana zata haifar da tarihi a tarihin siyasar kasar.