Shugban kungiyar yan kwadago ta NLC, Ayuba Wabba, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya zata bayyana adadin karancin albashin da maaikatan kasar zasu fara samu bayan da ta rahoto da kwamitin kungiyar kwadago ta mika mata.
Kungiyar ta cinma matsaya game da batun albashin a rahoton da kwamitinta ta mika ma shugaba Muhammadu Buhari.
Shugaban kungiyar ya bayyana hakan ne yayin da ya tattauna da manema labarai a garin Abuja ranar Litinin 8 ga watan Oktoba.
“Ina mai tabbatar wa ma’aikatan Nijeriya cewar an kamala duk wani shiri kan batun Karin albashi, yanzu haka an mika rahoto kuma za a saka masa hannu cikin wannan satin" inji shugaban kungiyar.
Ya milka godiyar sa ga sauran kungiyoyin ma'aikata na kasar da suka amince da biyan albashin da aka tsayar.
Sai dai bai bayyana adadin kudin da kwamitin kungiyar ta tsayar.
Tafiya yajin aiki
Idan ba'a manta ba a makon da ya gabata ne kungiyoyin kwadago na kasa zuka janye yajin aiki da suka tafi bayan da suka cinma matsaya da gwamnati.
Kungiyoyin sun dauki matakin ne domin nuna bacin ransu game da batun albashi mafi karanci na ma'aikata dake kasar wanda gwamnatin tarayya ta kaddamar amma bata fara aiwatar da tsarin ba.
NLC tace an dauki matakin zuwa yajin aikin ne bayan wa'adin da suka baiwa gwamnatin tarayya na tsawon kwana 14 domin duba lamarin albashi mafi karanci.