Gwamnan jihar Adamawa, Muhammadu Jibrilla Bindow ya nasarar zama dan takarar gwamnan jamiyar APC a jihar Adamawa.

Bindow ya doke kanin uwargidan shugaban kasa, Halilu Ahmed da kuma tsohon shugaban hukumar EFFC, Nuhu Ribadu, wajen zama dan takarar APC a zaben 2019.

Shugaban kwamitin zaben jihar Adamawa na jam'iyar, Ahmed Jibrin ya sanar dashi a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar.

Shugaban ya sanar da haka ne a safiyar ranar Lahadi 7 ga watan Oktoba inda yace gwamnan ya samu kuri'u 193,656 yayin da sauran abokan takarar sa suka samu 15,738  da  8,364.