Dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019 dake gabatowa karkashin jamiyar ANN, Fela Durotoye, ya zabi yar arewa, Hajiya Khadija Abdullahi Iya a matsayin abokiyar takarar shi.

Durotoye ya sanar da labarin haka ne a shafin sa na twitter ranar laraba 21 ga watan Nuwamba.

Kamar yadda ya bayyana, Hajiya Khadijah ta kware  a bangaren tallafa wa jama'a inda tayi sama da shekaru 10 tana bayar da gudumawa ga al'ummar.

Fela Durotoye picked Khadijah Abdullahi-Iya as his running mate
Fela Durotoye picked Khadijah Abdullahi-Iya as his running mate

Wa cece Khadijah Abdullahi Iya

Hajiya Khadijah Abdullahi Iya diya ce ga Alhaji Audu Bida wanda aka fi sani da Alhaji Audu Kongila da Hajiya Aisha Sherriff Usman.

Yar asalin karamar hukumar Bida dake jihar Neja amma haifafiyar yar Kaduna ce.

Tayi karatun digirin ta na farko a jami'ar Abuja inda tayi karatun ilimin shari'a. daga nan kuma ta kara karatun digiri ta biyu a jami'ar Jos shima a kan ilimin Shari'a.

Ta kafa cibiyoyi da gidauniyoyi domin tallafa ma karatun yara mara sa galihu a Kaduna da Abuja.