Babban bankin Nijeriya ta fitarda sabon sanarwa na hana likin kudi a wajen shagalin biki.
Sanarwar da wani kwamitin babban bankin ta fitar ranar Alhamis, ta shaida cewa za'a kaddamar da wasu jami'ai wadanda zasu ringa rangadi domin kama tare da gurfanar da masu yi ma kudin Nijeriya cin fuska.
Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, mai magana da yawun bankin, Isaac Okorafor, ya tabbatar da cewa za'a baza jami'an masu rangadi a jihohi dake fadin kasar kuma zasu gudanar da aikin sa-ido tare rundunar yan sanda da taimakon ma'aikata na ma'aikatar shari'a.
Ya ja kunnen yan Nijeriya cewa suyi hattara a wajen biki domin jami'ai zasu hallara domin lura da masu aikata laifi.
Kakakin ya kuma yi gargadi na baki su dukufa wajen baiwa iyayen biki kyautar kudi ko makamancin haka a cikin takardar sirri.
Sanarwar ta kara da cewa masu yin rubutu a saman kudi zasu fuskanci hukunci dauri na wata shidda ko biyan diyar N50,000.
Bugu da kari babban bankin zata dau mataki ga masu siyar da kudi domin liki a wajen biki.