Dan majalisar dattawa mai saman gado, Shehu Sani, ya kara zama dan takarar jamiyar APC na takarar dan majalisar dattawa a zaben 2019.
Uwar jam'iya ta kaddamar dashi a matsayin wanda zai wakilci APC a zaben 2019 ranar talata 2 ga watan Oktoba.
Jam'iyar ta amince da takarar shi a bisa sauran yan takara hudu dake neman kujerar wakilin yankin kaduna ta tsakiya a majalisa.
Shehu Sani ya samu fifiko fiye da sauran yan takara hudu da suka fito takarar karkashin jam'iyar.
Sai dai rahotanni daga jihar Kaduna na nuna cewa yan'yan jam'iyar na jihar sun gudanar da zanga-zangar nuna bacin ransu bisa ga matakin da uwar jam'iya ta dauka na kaddamar da Sani a matsayin wanda zai fito takara.
A labarin da jaridar Premium times ta fitar, jama'a sun kai koken su babban ofishin jam'iyar dake nan garin Kaduna.
Tun ba yau ba yau ba dan majalisar da gwamna Nasir El-rufai suka raba gari a harkar siyasa.
Bisa ga rasjhin jituwa dake tsakanin su wasu ke ganin cewa gwamnan ya mara ma Uba Sani baya na maye gurbin sanatan a zaben dake gabotowa. Sai dai hakan bata samu ba duba da matakin da jam'iyar ta dauka.
Sauran yan takara da suka fito takarar majalisar datawa karkashin APC sun hada da Shamsudeen Shehu Giwa, Uba Sani, Mohammed Sani Saleh da Usman Ibrahim.