ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

An soke zaben fidda gwani da aka yi a jihar Zamfara

Kwamitin ta soke zaben ga bisa ga sakamakon magudi da tabarbarewar tsaro a dai dai lokacin da aka zabe.

Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara

Shugaban Kwamitin zaben, Farfesa Abubakar Fari, wanda ya yi jawabi ga `yan jarida a hedikwatar `yan sandan jihar Zamfara, yayi zargin cewa akwai matsaloli da dama wadanda suka jibanci magudi da tsaro da suka dabaibaye zabe, kuma babu abin da ya fi dacewa face soke shi.

A cewar shugaban kwamitin  akwai wasu ma'aikatan gwamnati da ma'aikatan zabe da suka karbe takardun zabe suka kuma cike sakamakon da suke so a sanar da mutane.

Wannan matakin ya fito ne a cikin wata takardar sanarwa da Shima kakakin jam'iyar APC ta kasa, Yekini Nabena, ya tabbatar da haka a cikin takardar sanarwa da ya fitar safiyar ranar Alhamis.

ADVERTISEMENT

Sai dai mai magana da yawun jam'iyar bai sanar da sabon rana da za'a sake gudanar da zabe a jihar.

Rahotanni daga jihar sun tabbatar da faruwar tashin hankali a wasu kananan hukumomi na jihar yayin gudanar da zabbukan.

Sai dai a nata bangaren, gwamnatin jihar Zamfara tace baza ta amince da matakin da kwamitin ta dauka. Ta zargi kwamitin da nuna wariya ga yan takarar.

Gwamna Abdul'aziz Yari ya ce zabe bai soku ba, hasali gwmnati za ta dora daga inda kwamitin zaben ya tsaya ba tare da bata lokaci ba.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT