Pulse logo
Pulse Region

Gangamin Atiku a Legas; Karshen mulkin kama-karya yazo

Duk da cewa ranar aiki gangamin ya kasance, wannan bai hana daruruwan jam'a fitowa kwar da kwartansu domin halartar taron yakin neman zaben jam'iyar PDP a filin Tafawa Balewa Square, wanda ya ninka filin da APC ta gudanar da nata taron kwanan baya.
Atiku’s PDP Lagos Rally
Atiku’s PDP Lagos Rally

A cikin tawagar dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar akwai mataimakin sa Peter Obi, shugaban yakin neman zaben shugaban kasa na PDP Bukola Saraki, shugaban jam'iya Uche Secondus, dan takarar gwamna a jihar Legas Jimi Agbaje da sauran magoya bayan PDP.

Masu hannu da shuni da suka yi jawabi a wajen taron sun bayyana matsaloli da kasar ke fuskanta karkashin mulkin shugaba Buhari ciki akwai gurbataccen harkar kasuwanci, rashin tsaro da kuma rashin aikin yi da sauran su.

Shugaban jam'iyar PDP, Uche Secondus, ya jaddada cewa PDP ta gano wata makarkashiya da jam'iyar adawa ta APC ke shiryawa domin yin magudi a zabe dake gabatowa. Ya kara da cewa PDP baza da bari hakan ta faru ba.

Yayi kira ga jama'a da su zabi PDP kuma su tsare kuri'ar su a ranar zaben.

Shima abokin takarar gwanin jam'iyar, Peter Obi yayi kira ga taron da su zabi PDP domin cinma cigaban harkar kasuwanci da takarar Atiku ta tsara.

A jawabin sa, Atiku Abubakar ya tunatar da jama'a batun samad da aikin yi a kasar. Yayi kira ga al'ummar jihar Legas da su zabe shi domin aiwatar da burinsa da samad da aikin yi tare da farfado da dukiyoyin jama'a a harkar kasuwanci.

Jama'a da suka halarci taron sun watse ne bayan kammala taken kasa. Hakazalika gangain ya haifar da cinkoso daga titin Awolowo zuwa nan Tafawa Balewa Square. 

Next Article