Shugaban maaikatan gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya lashe zaben fidda gwani na jamiyar APC na zama dan takarar majalisar dattawa mai wakiltan kudancin jihar a zaben 2019.
Alhaji Bello Mandiya ya zama gwanin jam'iyar bayan da ya samu kuri'u mafi rinjaye fiye da sauran abokan takarar sa.
Baturen zaben, Alhaji Yakubu Hadejia, ya kaddamar dashi a matsayin wanda yayi nasara ranar Alhamis 4 ga watan Oktoba a garin Funtua.
Baturen yace wakilai daga kananan hukumomi sha daya da suka kunshi yankin mazabar suka kada kuri' a na zaben.
Alhaji Bello Mandiya ya fito takarar kujerar tare da tsohon kwamandan NYSC, Birgediya janar Maharazu Tsiga, da Nura Khalil, da Murtala Abu, da Faruk Lawal-Jobe, da Alhaji Garba Usman.
Hadimin gwamna Masari ya samu galaba a zaben bayan da ya samu kuri'u 1,469 cikin 3,400 da aka kada.
Sakamakon kuri'un da aka jefa na zaben ya fito kamar haka:
Nura Khalil (618), Tsiga (39), Abu (3), Usman (6) sai kuma Lawal-Jobe wanda ya samu kuri'u (1040). An kuma sauke kuri'u 233 da aka kada.
Yayin da ya zanta da manema labaru jim kadan bayan sanar da sakamakon zaben, Mandiya ya jinjina ma jam'ar yankin musamman wakilai da suka kada kuri'a.
Yayi alkawarin aiki da sauran yan takara wajen cinma burin jam'iyar APC a zaben 2019.
Daya daga cikin abokan takarar sa, Nura Khalil, ya taya shi murna tare da yin kira ga magoya bayan shi wajen bada hadin kai domin cigaba jam'iyar a zaben 2019.