Dan majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya mayar ma shugaba Muhammadu Buhari martani kan zargin da yayi a kasar Faransa kan cewa ya kwashi kudin jiha wajen yin yakin neman zabe a shekarar 2015.

A ziyarar aiki da ya kai birnin Faris kwnan baya, shugaba Buhari ya shaida ma yan Nijeriya dake kasar cewa gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya kammala ayyukan da Sanata Kwankwaso ya bari bayan da ya kwashe kudin jihar ya yi yakin neman zaben shugaban kasa a 2015.

Hirar shi da gidan rediyon Dala Fm ranar Litinin 26 ga watan Nuwamba, kwankwaso ya bayyana cewa shugaban bai da masani game da yadda ake tafiyar da ayyukan mulki a  jihar Kano.

Yana mai cewa "Ba zan ce komai a kan wannan zargi ba saboda shugaban kasa bai san komai a kan yarda muka tafiyar da mulki a Kano ba.

"Mutane da yawa sun zo sun gaya min abin da shugaban kasa ya fada. Har bidiyon kalaman da ya yi suka kawo mini. Abin da ya sa ba zan ba shi amsa ba shi ne, ya yi maganganunsa ne kawai wadanda ya ji daga wurin mutanen da ke kewaye da shi. Bai san komai a Kano ba."

Shugaban akidar Kwankwasiyya yana zargin cewa wadanda ke kusa da shugaba Buhari da zuga shi domin bata sunan shi a wajen shugaban.

"sun je suna gaya masa cewa ni dan ta'adda ne, ba na son Buhari. Amma ina so ku sani cewa duk cikin wadannan mutane ba wanda yake son Buhari kamar ni domin ni na taimake shi  ya ci zabe," inji shi.

Ya kara da cewa  Gwamna Ganduje bai ci gaba da ayyukan da ya fara ba, yana mai cewa dukkan ayyukan da ya ci gaba da aiwatarwa "na gwamnatin Shekarau abokin Buhari ne."

Game da bidiyon dake zargin gwamnan Kano da karbar cin hanci kwankwaso yana mai cewa  "Kafin a fitar da bidiyon na samu labari, amma na ce kar su sake shi. saboda abin kunyar ba kawai na iyalin gwamna ba ne, abu ne da ya shafi martabar mutanen Kano da addininsu da kuma kujerar da na rike mai alheri."

Ya sha alwashin sauya gwamnatin yanzu a zaben gwamnoni dake gabatowa.