Pulse logo
Pulse Region

"Yakar cin hanci ya zama dole" Buhari ya sanar ma Thabo Mbeki

Shugaban ya shaida ma tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu, Thabo Mbeki, yayin da ya kawo masa ziyara a fadar sa dake Abuja ranar Alhamis.
___8940774___2018___10___5___11___buharisallau_41780975_691180161256525_1475416045084237309_n
___8940774___2018___10___5___11___buharisallau_41780975_691180161256525_1475416045084237309_n

Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida cewa gwamnatin sa zata cigaba da yakar cin hanci da rashawa.

Shugaban ya shaida ma tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu, Thabo Mbeki, yayin da ya kawo masa ziyara a fadar sa dake Abuja ranar Alhamis 4 ga watan Oktoba.

Mbeki wanda shine shugaban fannin dake sa'ido ga hanyoyin shiga da fitar kudade a Afrika na kungiyar kasashen Afrika ya ziyarci shugaba Buhari domin sanar dashi game alamuran dake faruwar karkashin fannin da yake jagoranta.

Buhari ya shaida masa cewa "ya zama dole mu yaki cin hanci" domin tana daya daga cikin dalilai da yasa har jama'a suka zabe shi.

Yayi ikirari cewa gwamnatin sa tana samun nasara a yakin da take yi.

Shugaban ya kuma jinjina ma Mbeki bisa aikin da yake yi na taimakon kasashen Afrika.

A jawabin sa, tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu ya jaddada cewa ya cin hanci ya zama annoba a yankin Afrika kuma ya zama dole ya sa ido ga hanyoyin da kudade ke shiga da fita domin kawo karshen ta.

Next Article