Dan sarkin kano, Yarima Aminu Sanusi, zai angwance nan da yan kwanaki inda ya fitar da hotunan kafin auren sa tare da masoyiyar shi kuma gimbiya mai jiran gado.

Yariman zai angwance ga amaryar shi Fulani Zainab Ali Bashir. Sai dai babu wani labari game da ainihin ranar bikin auren tasu.

Ya sanar da haka a shafin sa na Instagram yammacin ranar talata tare da kayatattun hotunan sa tare da amaryar mai jiran gado.

Ya kuma rubuta sako mai narkar da zuciya mai cewa "Babu wani abu mai suna mata nagaro ko aure nagari. Abun da ya kamace mu shine muyi fatan samun mata ladabi da fahimta. Bayna shekaru da yin gwaji na ci karo da zinariya ta.  jama'a ina mai gabatar maku da sabuwar gimbiyar kano, Fulani Zainab Ali Bashir."