Gwamnatin jihar Kaduna dake karkashin jagorancin Mallam Nasir El-rufai ta sassauta dokar hana fita na saa 24 da ta saka.

An saka dokar ne ranar Lahadi 21 ga watan Oktoba sakamakon rikici dake neman barkewa a wasu unguwanni dake jihar.

Bayan taron majalisar tsaro da gwamnan jihar, Mallam Nasir El-rufai, yayi da wasu jami'an tsaro da sarakunan gargajiya na jihar, gwamnatin jihar ta daga dokar da ta saka a wasu ungwanni dake garin Kaduna.

An sassauta dokar ne domin baiwa al'umma damar gudanar da zirga-zirgar su na yau da kullum.

Kamar yadda gwamnatin jihar ta sanar a shafin ta na Twitter, al'ummar garin Kaduna zasu iya fita tsakanin karfe daya na rana zuwa karfe biyar na yamma.

Sai dai sanarwar ta bayyana cewa har ila yau dai dokar hana fita zata cigaba da aiki a wasu ungwanni dake garin.

Ungwannoin sun hada da Kabala west, Kabala Doki, Sabon tasha, Narayi da Maraban rido.

Sanarwar ta kuma ce an rage tsawon sa'o'in hana fita a yankunan Kasuwan Magani da Kujama, wuraren da rikicin ya samo asali.

Daga kaeshe sanarwar ta ce bayan karfe biyar na yamman yau Talata, za a koma kan tsarin hana fita na sa'a 24 har illa ma sha Allahu.