Gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da wasu sarakunan gargajiya dake jihar bisa ga zargin da ake masu na alaka da barayin shanu da masu satar mutane.

Kamar yadda kwamishnan kananan hukumomi na jihar, Alhaji Bello Dankande, ya shaida an kama hakimai uku sanan na hudun ya gudu.

A labarin da BBC hausa ta ruwaito, kwamishnan yace za a gudanar da bincike kan hakiman sannan a tube rawunan da ke kansu "kafin a gabatar da su a gaban shari'a."

Yace "Duk wani basaraken da ka ga mun dakatar, mun samu labari yana mu'amala da wadannan 'yan ta'adda. Misali, akwai wani uban kasa da aka kawo mana korafi a kansa cewa, na daya, ya tura galadimansa ya karbi belin barayi daga hannun 'yan sanda."

"Haka kuma ya karbi kudi daga hannun wani dan ta'adda. Mutanen garin sun zo sun ce ya karbi N50,000," inji kwamishnan.

Lamarin dai ya biyo bayan kwanaki da sakin yan mata tagwaye da barayi suka sace a jihar wanda ya jawo muhawa a kafafen watsa labarai.

Matsalar barayin shanu da masu satar mutane domin karbar kudin fansa a jihar Zamfara ya zama ruwan dare inda a wasu lokutan barayin suke kashe mutanen da suka sace.