Pulse.ng logo
Go

Ado Bayero Tsohon sarkin Kano ya cika shekara hudu da rasuwa

Marigayin ya rasu ranar juma'a 6 ga watan Yuni na shekarar 2014 bayan wata gajeruwar rashin lafiya da yayi.

  • Published:
Tsohon sarkin Kano ya cika shekara hudu da rasuwa play

Alhaji Ado Bayero ya rasu ranar 6 ga watan Yuni na 2014

(BBCHausa)

Yau Laraba tsohon Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero yake cika shekara hudu da mutuwa.

Marigayin ya rasu ranar juma'a 6 ga watan Yuni na shekarar 2014 bayan wata gajeruwar rashin lafiya da yayi.

Kafin rasuwar sa, marigayin ya shafe tsawon shekaru 51 kan gadon mulkin Kano.

A tarihin kasar hausa yana daya daga cikin sarakuna mafi daraja da karfin iko kuma shine sarki mafi tsawon shekaru a kan gadon sarautar mulki.

Alhaji Ado Bayero wanda aka nada da sarautar Kano a cikin jamhoriyar farko na shekarar 1963 ya rasu yana da shekaru 83 a duniya.

Tsohon sarkin Kano ya cika shekara hudu da rasuwa play

Marigayi tsohon sarkin Kamo Alhaji Ado bayero

(Instagram/aminuadobayero)

 

Marigayi yana daya daga cikin sarakunan gargajiya da suka yi tsayin daka wajen farfado da martaban kasar hausa ga bainar jama'a duba da yadda yake jagorantar hawan daba wanda ke janyo jama'a da dama daga kasashen duniya daban-daban.

kafin ya hau gadon mulki, yayi aiki a matsayin jami'in dan sanda kuma yayi aiki a matsayin ma'aikacin bankin da aikin diflomasiya inda ya zama jakadan Nijeriya zuwa kasar Senegal.

Ya rasu ya bar yara da jikoki, cikin yaran shi akwai Wanban Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.

 

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.