Pulse.ng logo
Go

Ziyara Shugaban Buhari zai kai ziyarar kwanaki hudu kasar Ingila domin ganin likita

Kamar yadda sanarwar ta bayanar, shugaban zai kai ziyarar ne ranar talata 8 ga watan yau bisa bukatar likitan shi

  • Published:
Shugaba buhari ya dawo daga kasar Amurka play

Shugaba buhari ya dawo daga kasar Amurka

(Instagram/buharisallau)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sake kai ziyarar kasar Ingila, sai dai a wannan lokacin zai yi kwananki hudu ne domin ganin likita.

Fadar sa ta sanar da haka a daren ranar litinin 7 ga watan Mayu.

Kamar yadda sanarwar ta bayanar, shugaban zai kai ziyarar ne ranar talata 8 ga watan yau bisa bukatar likitan shi.

Sanarwar, wanda Garba Shehu ya fitar, ya kara da cewa  shugaban ya gana da likatan shi sanda jirgin sa ya yada zango a birnin London hanyar shi na dawowa Nijeriya daga birnin Washington.

Shugaban zai dawo Nijeriya a karshen mako inda bayan dawowar shi zai kai ziyarar aiki jihar Jigawa.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.