Pulse.ng logo
Go

Moda Shahararren jarumi yana fama da rashin lafiya

Saratu Gidado da Hamisu Iyantama da shugaban hukumar tantance fina-finai ta jihar kano sun kai masa ziyara a asibitin da yake jinya a garin kaduna

  • Published: , Refreshed:
Jaruma Saratu Gidado ta kai masa ziyara a asibitin da yake jinya play

Jaruma Saratu Gidado ta kai masa ziyara a asibitin da yake jinya

(Instagram/saratudaso)

Shahararren tsohon jarumin dandalin fina-finan hausa Sani Idris wanda aka fi sani da Moda ya jinyar rashin lafiya a wata asibiti dake jihar kaduna.

Jarumin shirin 'Wasila' ya shaharen a fagen masana'antar Kannywood musamman a yanayin ire-iren matsayin da yake fitowa. Ya shahara ne a fitowa a matsayin mai ruruta gaba a fina-finai.

Jaruma Saratu Gidado ta kai masa ziyara a asibitin da yake jinya play

Jaruma Saratu Gidado ta kai masa ziyara a asibitin da yake jinya

(Instagram/saratudaso)

 

Kamar yadda jaruma Saratu Daso ta sanar a shafin ta na Instagram yayin da ta kai masa ziyara a asibitin da yake kwance, jarumar ta sanar cewa yana fama da ciwon suga wanda aka kira da Diebetes a turanci.

Banda saratu Daso, shugaban hukumar tantance fina-finai na jihar kano,  Alhaji Isma'il Afakalla tare da tsohon jarumi Hamisu Iyantama, sun kai ziyarar duniya ga tsohon jarumin a asibitin da yake jinya.

Tsohon jarumi, Hamisu Iyantama da shugaban hukumar tantance fina-fina ta jihar Kano sun kai masa ziyara play

Tsohon jarumi, Hamisu Iyantama da shugaban hukumar tantance fina-fina ta jihar Kano sun kai masa ziyara

(Instagram/iyantama)

 

Tun ba yau ba Moda ke fama da wanan rashin lafiya, muna masa fatan samun sauki cikin gaggawa.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement