Pulse.ng logo
Go

Tafsirin Ramadan Shugaba Buhari ya jagoranci ma'aikatan fadar sa wajen sauraron karatun tafsiri

Shugaban ya halarci wajen karatun a masallacin dake fadar sa don raya wata mai albarka ta Ramadan.

  • Published:
Shugaban kasa a wajen karatun tafsiri play

Shugaban kasa a wajen karatun tafsiri

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tare da sauran alúmmar musulmai dake fadar sa wajen sauraron karatun tafsiri.

Shugaban ya halarci wajen karatun a masallacin dake fadar sa don raya wata mai albarka ta Ramadan.

Yayin gabatar da karatun, limamin masallacin fadar shugaban, Abdulwaheed Abubakar, yayi godiya ga Allah dangane da saukin da ya samu na rashin lafiya da yayi wanda ya sa shugaban ya azumci watan ramadan a kasar waje bara.

Shugaban kasa yayin da yake sauraron karatun tafsiri a masallacin fadar sa play

Shugaban kasa yayin da yake sauraron karatun tafsiri a masallacin fadar sa

Sakon shugaban gabanin ganin watan Ramadan

A jawabin sa don taya musulmai murnar shiga watan azumi ta Ramadan, shugaba Buhari ya kwadaita yan Nijeriya da suyi amfani da wannan watar wajen nuna juna kauna tare da suyi koyi da halin fiyayyen halita wajen kyautata ma yan uwa.

"Ina jan hankalin al'ummar Musulmi kan cewa Azumi ba wai ya takaita ba ne wajen rashin ci da sha amma wata dama ce daga Ubangiji na tsarkake zuciya da yiwa kai hisabi.

 Kuma Ina neman Musulmi su kara nuna kauna da tausayawa juna kuma a samun kowa ne a lokacin Azumi, Manzon Allah yana rubanya kyautar da yake yi don haka Ina kira gareku kan yin koyi da wannan hali da Manzon Allah.

 Ina fatan Ubangiji Ya ba mu karfin kammala wannan Azumi cikin nasara", yace.

Tabbatar da ranar farkon wata

Ranar farko ga watan Ramadan ya fara ne ranar alhamis 17 ga watan Mayu a mafi yawancin kasashen duniya bayan tabbatar da ganin jinjirin watan.

A Njieriya, sarkin Musulmai, mai alfarma Alhaji Abubakar Sa'ad na uku ya tabbatar da ganin watar a wasu jihohi na kasar.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.