Pulse.ng logo
Go

Gwamnati ta rage kudin jarabawar JAMB da Neco

Sabon tsarin kudin jarabawar zata fara aiki daga watan Janairu na 2019.

  • Published:
Olisa Agbakoba asks NASS to override Buhari’s veto on Electoral Bill play

President Muhammadu Buhari

(NAN)

Gwamnatin tarayya ta dau matakin rage kudin fom din jarabawar neman shiga jami'a ta JAMB da NECO.

Labarin haka ya fito ne ranar Laraba 28 ga watan Nuwamba inda mai yi ma shugaba Buhari hidima kan kafofin watsa labarai, Bashir Ahmad, ya sanar a shafin sa na Twitter.

An canza kudin jarabawar JAMB daga N5,000 zuwa N3,500. Hakazalika jarabawar NECO maimakon N11,350 yanzu kudin ta koma  N9,850.

Gwamnatin tarayya ta dau matakin ne bayan kammala taron majalisa na mako-mako da ta saba yi wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Ministan ilimi, Adamu Adamu, ya shaida wa manema labarai bayan taron cewa an dauki matakin ne bayan korafe-korafe da iyaye keyi kan tsadar fom din jarabawa.

Sabon tsarin kudin jarabawar zata fara aiki daga watan Janairu na 2019.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement