Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, yace idan yayi nasarar zama shugaban kasa ba zaiyi jinkiri wajen kaddamar da ministocin majalisar sa.

Atiku yayi raddi ga gwamnatin shugaban Buhari wanda aka kaddamar bayan wata shidda da rantsar dashi saman kujerar mulkin kasa.

Yace idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa kafin ranar 29 ga watan Mayu zai kaddamar da majalisar sa.

A bisa bayanin Atiku Najeriya na bukatar shugaba nagari wanda zai farfado da ki'imar ta.