Shehin malami dake zama a Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, yayi karin haske game da ziyarar da ya kai tare da dan takarar shugaban kasa zuwa gidan Olusegun Obasanjo.

A ranar Alhamis ne dan takarar PDP, Atiku Abubakar, ya kai ma tsohon ubangidan sa ziyara domin sasanta tsakanin su tare da neman goyon sa a zaben 2019.

Alhaji Atiku ya ziyarci gidan tsohon shugaban kasan ne tare da wasu jiga-jigan jam'iyar sa tare da wasu fitattun malaman addinin kirista da na islama.

Sheikh Gumi yana daga cikin malaman da suka kai ziyarar sai dai labarin ziyarar tasa ya haifar da cece-kuce ga yan Najeriya. Wasu na ganin cewa malamin ya fara bangar siyasa tare da nuna goyon baya ga dan takarar PDP.

Hirar shi da BBC haysa malamin yayi karin haske game da lamarin  inda ya nuna cewa ziyarar na daga irin koyarwar Manzon Allah.

Sheik Gumi ya ce Manzon Allah ya taba cewa yana matukar maraba da duk wata gayyata na yin sulhu ko da tsakanin wanda ba Musulmi ba ne. Ya kara da cewa idan har shugabanni na cikin zaman lafiya, to ana sa ran kasa ma za ta kasance cikin zaman lafiya.

Malamin ya kuma yi karin haske a kan zargin da ake cewa ko suna nuna goyon bayansu ne ga takarar Atiku Abubakar, inda ya ce ' Ba a Atiku Abubakar ba, ko wanene koda a misali shugaba Muhammadu Buhari zai fito ya ce zai yi sulhu da kanal sambo Dasuki da aka kulle, a nemi ni a ce na zo nayi sulhi, to zan yi'.

Daga karshe Sheikh Gumi ya kawar da zargi da ake yi na cewa yana goyon bayan dan takarar shugaban kasa.

Yace, shi fa a bangarensa ba ya goyon kowa a takarar shugabancin kasa, domin ko iyalansa ma ba zai ce musu ga wanda za su zaba ba, don haka shi ba shi da zabi, kuma kowa na da na sa zabin.