Pulse.ng logo
Go

Yan mata tagwaye da aka sace a zamfara yayin da suke shirye-shiryen auren su

Barayin sun sace Hassana da Husainan ne a garin Dauran dake karamar hukumar Zurmi na jihar Zamfara a karshen makon da ya shude.

  • Published:
play Barayin sun bukaci a biya su naira miliyan 100 kafin su sake su. (Instagram/northern_blog)

Al'ummar jihar Zamfara na kewa yayin da wasu barayi suka sace tagwaye wadanda ake shirye-shiryen bikin auren su.

Masu garkuwan sun sace Hassana da Husainan ne a garin Dauran dake karamar hukumar Zurmi na jihar.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, an sace tagwayen ne tdakanin ranar Asabar da Lahadi na makon da ya shude.

Mataimakin shugaban karamar hukumar Zurmi, Abubakar Muhammad, ya shaida ma BBChausa cewa masu garkuwan sun bukaci a biya su Naira miliyan 100 kafin su sako tagwayen.

Yace tagwayen suna cikin mutane bakwai daga karamar hukumar da barayi suka sace kwana-kwanan nan.

Abubakar yayi kira ga yan Najeriya da su kawo masu dauki domin kawo karshen matsalar da suke fuskanta.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement