Pulse.ng logo
Go

Gasar AMMA Ali Nuhu da Haliam Atete sune gwarzayen bana

Taron gasar na bana wanda shine karo na biyar ya gudana ne a dakin taro dake nan Soli Center a garin Katsina.

  • Published:
Jaruma ta amshi kyautar gwarzuwar shekara play

Jaruma ta amshi kyautar gwarzuwar shekara

(Instagram/haleemaatete)

Fitattun jarumai Ali Nuhu da Halima sun lashe kyautar gwarzayen shekara a gasar AMMA.

Jaruma Halima Atete ta samu kyautar gwarzuwar shekara yayin da shi sarakin kannywood, Ali Nuhu ya amshi kyuatar gwarzon mai bada umarni bisa rawar da ya taka a fim din "Mansoor".

Halima Atete tare da Kawu Kamfa play

Halima Atete tare da Kawu Kamfa

(Instagram/haleemaatete)

 

Shima Umar M.Sheriff ya samu kyautar matashin jarumi mai tashe a gasar bana bisa nuna basira da yayi a cikin shirin Mansoor.

Ali Nuhu da Umar M.Sheriff sun amshi kyauta bisa rawar da suka taka a shirin Mansoor play

Ali Nuhu da Umar M.Sheriff sun amshi kyauta bisa rawar da suka taka a shirin Mansoor

(Instagram/realalinuhu)

 

Arewa Music and movies award gasa ce wacce take karrama fitattun yan wasan fim da masu harkar fim tare da mawaka da suka yi fice a ko wani shekara.

An fara gasar ne a cikin shekarar 2014 kuma kamfanin CEMS take daukar nauyin shirya ta.

Taron gasar na bana wanda shine karo na biyar na gasar, ya gudana ne a dakin taro dake nan Soli Center a garin Katsina.

Taron ya samu halarcin dinbim jarumai da mawaka da masu ruwa da tsaki a masana'antar fina-finai. Jarumai da dama sun samu kyaututuka bisa rawar da suka taka a masana'antar nishadantarwa ta arewa.

Ku kasance tare da mu domi samun karin bayanio game da yadda gasar ta kaya tare da jarumai da suka samu mafi yawancin kyauta.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.