Bayan tayi bita kan lamarin, gwamnatin tarayya ta kara karancin albashin maaikatan Nijeriya daga naira dubu sha takwas (N18,000) zuwa naira dubu ashirin da hudu (N24,000).

Babban ministan kwadago Chris Ngige ya sanar da haka yayin da ya gana da manema labarai bayan kammala zaman majalisar koli ranar Laraba 10 ga watan Oktoba.

Kamar yadda ya bayyana da farko kungiyar yan kwadago na kasar ta kaddamar da N30,000 a matsayin sabon albashin da take so a biya ma'aikata bayan ta janye yajin aikin da ta tafi amma a wani bangare kuma gwamnoni basu amince da haka inda suka ce baza su iya biyan haka ba.

Ministan ya jaddada cewa muhimmin abun dubawa game da yarjejeniya kan batun albashin ma'aikata shine tabbatar da cewa gwamnati zata iya biyan kudin da aka tanadar a dai-dai lokacin da ya kamata a biya ma'aikata.