Jirgin sama ya samu hatsari yayin da sojoji ke shirin tafka ma Boko haram hari
Shugaban fannin watsa labarai na NAF Air CommodoreOlatokunbo Adesanya ya sanar da haka a wata takardada ya fitar.
kakakin ya tabbatar cewa babu wanda ya rasu sakamakon hatsarin
"Babban hafsan sojojin sama na kasa ya bada umarni na gaggawa na kafa yan bincike domin gano silar hatsari kamar yadda ake yi a fadin duniya.
har yanzu kuma NAF tana kira ga jama'a da su cigaba a goyon bayan rundunar sojoji yayin da suke kokarin tabbatar da tsaro ga yan kasa da ma kasar baki daya" kamar yadda aka rubuta a takardar da kakakin ya fitar.
Makamancin haka ya faru a 2017
A cikin watan Yuli na bara wani jirgin sama na sojoji ya samu hatsari inda har ta fada cikin ruwa a wani bangaren arewa maso gabas na kasar.
Hakazalika cikin watan Agusta na 2017, wani jirgin rundunar NAF ya samu hatsari a garin Kaduna yayin da take kan aiwatar da wata gaggarumar aiki kamar yadda Air commodore Olatokunbo Adesanya ya sanar.