Shugaban yayi nadin ne ranar alhamis 24 ga watan mayu.
Ga sunayen sabbin jami'an da ya nada tare da hukumar su kamar haka:
Dokta Anasa Ahmad Sabir - an nada shi a matsayin babban daraktan asibitin koyarwa ta Jami'ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto.
Dokta Theresa Obumneme Okoli wadda ya nada a matsayin sabon shugaban kwalejin gwamnatin tarayya dake horas da malamai dake nan garin Umunze na jihar Anambra.
Sai kuma Dokta Emmanuel Ikenyiri wanda ya nada a matsayin shugaban Kwalejin Gwamnatin Tarayya dake horas da malamai na garin Omoku a jihar Rivers.
Wannan sabbin nade-nade da yayi ya biyo bayan wanda ya yi a farkon watan mayu. Shugaban yayi nade-naden ne a hukumar NDIC da kuma hukumar zabe ta kasa.
Cikin wadanda ya nada a hukumar NDIC akwai babban lauya, Festus Keyamo wanda ya kaddamar a matsayin kakakin yakin neman zaben sa.