Advertisement

Yan majalisar wakilai 36 sun fice daga APC zuwa PDP da ADC

Mutum 32 sun fice zuwa PDP yayin da sauran mutane 4 suka koma jam'iyar ADC wanda tafiyar Obasanjo ta kafa.
Advertisement

Guguwar canji na cigaba da dukar jamiyar APC yayin da wasu yan majalisar wakilan tarayya su 36 suka sauya sheka zuwa jamiyar adawa ta PDP da ADC.

Advertisement

Kakakin majalisar Yakubu Dogara ya karanta labarin haka a a zaman majalisar da aka gudanar ranar talata 24 ga wata.

Mutum 32 sun fice zuwa PDP yayin da sauran mutane 4 suka koma jam'iyar ADC wanda tafiyar Olusegun Obasanjo ta Coalition for Nigeria Movement ta kafa.

Labarin ficewar su ya biyo bayan wanda ya faru a zauren majalisar dattawa inda sanatoci 15 suka sauya jam'iya daga APC zuwa PDP.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement