Advertisement

Bayan ziyarar aiki da ya kai Morocco shugaba Buhari ya dawo gida

Shugaban ya ziyarci kasar ne ranar lahadi domin amsar gayyatar da sarkin kasar yayi masa.
Advertisement

Da dawo garin Abuja yamacin ranar litinin 11 ga wata inda manyan ma'aikatan gwamnatin sa suka tarbe shi yayin da ya sauka daga jirgi.

Advertisement

Saukar sa kasar, shugaban ya samu kyakkyawar tarba daga mai alfarma sarki Muhammadu na shidda wanda ya birge wanda tashoshin watsa labarai na kasar su takwas suka watsa kai tsaye.

Muhimman batutuwa da suka tattauna a kai sun hada da samun matsaya kan yarjejjeniyar inganta masana'antar takin zamani. Hakalizaka zasu tattauna kan samad da ingantaccen tsarin ilimi da hanyoyin tsarrafa iskan gas da sauran ma'adanai kimiya.

Shugaban dai ya ziyarci kasar tare da gwamnan jihar Ebonyi David Umahi da takwaransa na jihar Jigawa AlhajiAbubakar Badaru tare da wasu manyan ma'aikatan gwamnatin sa.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement