Tsohon minista ya rushe rijiyoyin da ya gina ma al'ummar sa bayan ya fadi zabe
Tsohon minista kuma tsohon dan majalisa a kasar Uganda Patrick Okumu-Ringa ya ruguza rijiyoyin tuka-tuka da ya gina ma mazabar shi sakamakon rashin nasarar shi a zaben da aka gudanar.
Tsohon dan majalisar wanda ya shafe tsawon shekaru 10 yana wakiltar mazabar Padyere County a majalisar, bai yi nasarar komawa zauren tun bayan faduwar shi a shekarar 2006.
A zaben da aka gudanar a kasar kwanan baya dan takarar shine yazo na uku a cikin wadanda ke neman kujerar wakilin shiyar inda ya samu kuri'u 1,270 cikin 9,940 na masu zaben.
A labarin da jaridar New Vision ta fitar, Patrick Okumu-Ringa ya gasgata abun da ya faru tare da jaddada cewa bai yi nadamar aikin da yayi. A cewar shi bai ji dadin sakayyar da mazabar shi suka yi masa don haka su nemi wata hanyar neman ruwa.
Yana mai cewa "Mutanen nan basa godiya. Kuri'ar su kawai na bukaci su su jefa mun. Na dau nauyin karatun yara da dama amma a ko da yaushe kira suke wai ban gudanar da aiki na azo-gani."
Aikin rushe-rushen rijiyoyin ya fara ne kwana uku bayan sanar da sakamakon zabe.