Advertisement

Manyan yan siyasa sun halarci jana'izar matar Janar Ali Gusau

Hajiya Binta ta rasu ne a wata asibiti dake birnin London ranar Juma'a 27 ga watan Yuli kuma gawar ta ya iso kasar ranar litinin.
Advertisement

Gwamnoni shidda suka halarci janaizar Hajiya Binta matar tsohon ministan tsaro kuma tsoho mai baiwa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro Janar Ali Gusau wanda ta rasu makon da ya shude.

Advertisement

Mariga'iyan ta rasu ne a wata asibiti dake birnin London ranar Juma'a 27 ga watan Yuli kuma gawar ta ya iso kasar ranar litinin.

Anyi jana'izar ta a babban masallaci dake titin Yahaya road nan garin Kaduna kana aka binne ta a makabartar dake nan unguwar Sarki.

Gwamnonin da suka halarci jana'izar akwai gwamnnoni jihar Kaduna, Adamawa, Nasarawa, Gombe, Nasarawa da Kano. Bayan ga haka tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shima ya halarci jana'izar.

Mataimakin gwamnan jihar Zamfara Ibrahim Wakala tare da sauran masu ruwa da tsaki a fannoni mabambamta sun halarci sallar.

Advertisement

Mataimakin gwamnan wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar Zamfara ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa ta gari wadda ta sadaukar da rayuwarta wajen bauta wa Allah. Ya kuma yi addu'ar Allah ya jikanta da rahama ya gafarta mata ya sa Aljannar firdausi ce makomar ta.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement