Advertisement

Liyafar bude baki da shugaba yayi da yan majalisar tarayya

An shirya liyafar ne a fadar shugaban tare da wasu manyan kusoshin majalisar dattawa karkashin jagorancin Bukola Saraki.
Advertisement

Kamar yadda labari ya bayyana yan majalisar tare da shugaban sun gudanar da sallar magrib a masallaci fadar shugaban gabanin haka suka garzaya dakin taro inda aka shirya liyafar bude bakin azumin ranar 8 ga watan Ramadan.

Advertisement

An shirya liyafar ne a fadar shugaban dake nan Abuja tare da wasu manyan kusoshin majalisar dattawa karkashin jagorancin shugaban ta, Bukola Saraki.

Manyan jami'aiu da suka halarci wajen liyafar sun hada da shugaban ma'aikata na shugaban, Abba Kyari da wasu ma'aikatan fadar shugaban.

A bangaren yan majalisun akwai, shugaban sanatoci, Ahmed Lawan da sauran goganin majalisar.

Sai dai babu wani karin bayani game da manufar hada liyafar ko wata tasirin da yin haka zai haifar.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement