Advertisement

Soja ya kashe kansa bayan ya halaka matar sa yayin da ya gano ainihin mahaifin yaran sa

Bayan binciken da yayi, ya gano cewa yaran ba nashi bane, wani abokin aikin sa ne wanda ke gaba dashi a matsayin yayi ma matar sa ciki.
Advertisement

Mummanr lamarin ya faru ne a barikin sojoji inda yake zama. Kamar yadda majiya suka ruwaito, sojan ya tunkari matar sa domin tabbatar da labarin da ya jiyo daga yan anguwa.

Advertisement

Haduwar su ke da wuya sai ta sanar masa cewa hakika ba shi bane mahaifin yaran, abokin aikin sa ne mahaifin su.

Nan take sojan ya harbe ta da bindiga har lahira kana daga baya ya kashe kansa yayin da ya ji labari cewa yan sanda na neman sa ruwa a jallo.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement