Dan ƙwallon Ƙungiyar Chelsea, zai bar su a watan Janairu
Dan ƙwallon Najeriya -Mikel Obi- wanda yake buga lambar tsakiya, ya sanar da mu cewa ya shirya ya tashi daga Ƙungiyar Chelsea a watan Junairu.
Wannan ya faru bayan Koci Antonio Conte ya ƙi yarda ya shigar da sunansa a cikin jerin sunayen waɗanda za su buga wasa.
Tun dawowansa daga wasan Olympis, wanda aka yi a ƙasar Rio Brazil, Koci na Chelsea ya hana Mikel wasanni. Za ku túna cewa Mikel ya taimake Najeriya ga cin lambar tagulla. Daga duk alama, Conte ya fi son haɗin gwiwa na NʼGolo Kante da Nemanja Matic a madadin Mikel.
Wannan rashin wasa yana ɓata ma Mikel Obi rai, kuma ya ámbata cêwa zai tashi daga Ƙungiyar taka Leda na Chelsea. Ɗan Kwallo Mikel, mai shekara ashirin da tara ya yi bayani da gidan talabijin na ESPN haka:
"Zan sa idò domin ganin yanda za mu kasance a watan Janairu. Tun lokacin da na fara wasan taka leda, ban taɓa samun irin wannan yanayi ba. Wajibi ne in tashi domin warware wannan matsalan da nake ciki."
"Wannan labari gaskiya ne, kuma ina ƙokari da horo domin ƙarin gwaninta. Ina yi ma Ƙungiyar Chelsea fatar Alheri, ina yi musu fatar saʼa. Ina farin-ciki da wasannin mu."
"Na jima sossai a ƙungiyar Chelsea. Na shaida zuwa da wucewa na Manajoji da dama. Wannan abinda ke faruwa ba abin mamaki ba. Na jima a ƙungiyar Chelsea. Idan watan Janairu ya shiga, zan ɗauki mátákín da ya dace."
Mikel Obi, ɗaya ne daga cikin ʼƴan kwallon da suka fi daɗewa a Ƙungiyar Chelsea.. Ya ci wasa na premier league so biyu, wasa na FA Cup so huɗu, Wasan Europe League so ɗaya, da kuma Champions League so ɗaya.