Advertisement

IPOB zata kaddamar gidan rediyo wanda ake watsa shirye-shiryen ta cikin harshen hausa

Za'a watsa shirye-shiryen tashar a ko wace rana bayan an kaddamar da ita ranar 6 ga watan Janairu
Advertisement

A wata takarda da kakakin kungiyar Emma Powerful ya fitar ranar Alhamis 4 ga watan Janairu ya sanar cewa tashar wanda za'a sanya mata suna "Radio Nigeria Hausa Service" zata kasance muryar IPOB domin kawar da cikas da masu kawo masu ci baya.

Advertisement

Powerful yace za'a fitar da shirye-shiryen tashar a ko wace rana bayan an kaddamar da ita ranar 6 ga watan Janairu dai dai karfe 7 na yamma.

Ya kara da cewa za'a kama shirye shiryen da za'a fitar a tashar a duk fadin Afrika domin zata kasance mafi sigina a nahiyar.

Duk wani yankin da ke da hausawa a nahiyar Afrika zata iya kama shirye-shiryen ta.

Shi dai kakakin ya daura da cewa wannan cigaba da kungiyar ta samu taska ce ta nuna ma mutane cewa manufar kungiyar shine yakin neman yanci.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement