Advertisement

Hafsat Idris: Hotunan bikin murnar zagayowar ranar haihuwar shahararriyar jaruma

<strong>Hafsat Idris</strong> ta shirya liyafa don murnar zagayowar ranar haihuwar ta tare da sauran yan uwa da abokan sana'ar ta.
Advertisement

Fitacciyar jarumar fim hafsat Ahmad Idris wacce aka fi sani da Hafsat barauniya tayi murnar cika shekaru 29 a duniya.

Advertisement

Jarumar mai tauraro tayi bikin zagayowar ranar haihuwar ta ranar 15 ga watan Yuli.

Don raya zagayowar wannan ranar farin ciki jarumar ta shirya taron liyafa tare da gayyatar yan'uwa da abokan sana'ar ta na masana'antar Kannywood.

Wasu daga cikin manyan jaruman kannywood da suka halarci taron bikin sun hada da Ali Nuhu, Ahmed Lawan, Nazir Dan hajiya, Abba Maishadda, Kamal S.Alkali.

Advertisement

A bangaren mata kuma Nafisa Abdullahi, Aisha Humaira.

Mawaki Umar M.Shereef ya nishadantar da baki da sabuwar wakar shirin "Ruwan dare". Shahararren mai gabatar shirin biki Mc Ibrahim Sharukhan ya jagorancin taron bikin.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement