Advertisement

Nijeriya da Nijar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar gina matatan mai a jihar Katsina

An gudanar da taron rattaba hannu ga yarjejeniyar a fadar shugaba Muhammadu Buhari dake nan babban birnin tarayya ranar talata 24 ga watan Yuli.
Advertisement

Shugabanin kasashen Nijeriya da jamhoriyar Nijar sun rattaba hannu ga yarjejeniyar gina sabon matatan mai a garin Mashi dake jihar Katsina.

Advertisement

Yarjejeniyar zai kara gina bututun man iskar dafa abinci wanda za'a jawo daga kasar Nijar zuwa Nijeriya kuma yarjejeniyar zai lakume dala biliyan biyu.

An gudanar da taron rattaba hannu ga yarjejeniyar a fadar shugaba Muhammadu Buhari dake nan babban birnin tarayya ranar talata 24 ga watan Yuli.

Takwaransa  na jamhoriyar Nijar Mamoudou Issoufou tare da wasu jami'an gwamnatin sa sun halarci taron.

Ministan mai Ibe Kachukwu tare da takwaransa na Nijar mista Foumakoye Gado suka sa hannu ga takardar yarjejeniya a madadin kasashen.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement