Advertisement

Ko kun san dan wasa da kasar da ta fara samun jan kati a gasar bana?

Wasan su da Japan ranar Talata, Carlos Sanchez, na Columbia ya amshi jan kati baya minti uku da fara wasa
Advertisement

Mai tsaron bayan tawagar yan wasan kasar Columbia shine dan wasan farko da ya fara samun jan kati a gasar cin kofin duniya na 2018.

Advertisement

Wasan su da kasar Japan ranar talata 19 ga watan Yuni, Carlos Sanchez ya amshi katin sakamakon sa hannu da yayi a daidai sanda dan wasan Japan ya nemi ya zurra kwallo a raga.

Wannan shine jan kati mafi sauri da za'a dan wasa a gasar kofin duniya a tarihi bayan wanda ose Alberto Batista na kasar Uruguay ya samu a gasar 1986.

Sakamakon barna da yayi, jagoran wasan ya hura ma Japan penarti wanda Shinji Kagawa bai wasa ba wajen mayar dashi abun farin ciki ga tawagar sa.

Wasan dai tashi 2-1 ga Japan bayan da Columbia ta kammala wasan da yan wasa goma.

Advertisement

Columbia da Japan da Senegal da Poland suna rukuni daya a gasar wanda ya fara tun makon da ya shude.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement