Advertisement

Ta gamu da ajalin ta sati daya bayan ta sallami mai gadin ta

Makwabta sun shaida cewa sun ji sanda matar take rokon yan fashin da su yi mata rangwami, sai dai basu samu ikon tunkarar barayin.
Advertisement

Yan fashi da makami sun dirar mata ne a gidan ta dake nan Citec estate na Abuja, inda suka caccaka mata wuka a kirji da wuya.

Advertisement

A bisa labarin da jaridar Punch ta fitar, yan fashin sun kai mata farmaki ne yayin da take kokarin kuna injin wuta na gidan.

Sai daga bayan yan fashin sun fita daga gidan ta suka garzaya domin duba lafiyar ta, sai dai suka gan ta a mace jinin ta nata malalowa.

Ba tare da bata lokacin jami'an tsaro sun gaggauta wajen bincike kan lamarin.

Daga bisani, Punch ta ruwaito cewa an cafke wasu da ake zargi da sa hannu game da kisan.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement