Advertisement

Buhari zai tafi hutun kwana 10 birnin London

Kamar yadda sanarwa ta bayyana mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo zai cike gurbin sa wajen tafiyar da alamuran shugabancin kasa yayin da shugaban ya tafi hutun.
Advertisement

Sako da ya fito daga fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari zai garzaya birnin domin yin hutun kwana 10.

Advertisement

Mai baiwa shugaban shawara kan watsa labarai Femi Adeshina ya sanar da haka inda yace shugaban zai bar Nijeriya ne ranar juma'a 3 ga watan Agusta.

Kamar yadda sanarwa ta bayyana mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo zai cike gurbin sa wajen tafiyar da alamuran shugabancin kasa yayin da shugaban ya tafi hutun.

Fadar shugaban ta bayyana a cikin sanarwar da ta fitar cewa kamar yadda kundin mulkin kasa ta tanadar shughaban ya tura wasika game da hutun zuwa ga zauren majalisar dattawa da na wakilai.

Wannan labari ya fito ne washe garin saukar shugaban garin Abuja bayan tafiyar da yayi zuwa kasar Togo domin halartar taron kungiyar ECOWAS.

Advertisement

Shugaban ya samu matsayin jagoran kungiyar bayan da kungiyar ta zabe shi domin sauya shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement