Advertisement

Gwamnatin tarayya tace ma’aikata su huta ranar litinin da talata

Minister of Interior, retired Lt.-Gen. Abdulrahman Dambazau
Minister of Interior, retired Lt.-Gen. Abdulrahman Dambazau
Babban ministan aiki gida Lt.-Gen. Abdulrahman Dambazau (Rtd.) yayi wannan sanarwar ranar alhamis a Abuja
Advertisement

Gwamnatin tarayya tace ranar litinin 26 ga watan Yuni da talata 27 ga watan Yuni ranakun hutu ne.

Advertisement

Bisa ga labarin gidan jarida Punch, an bada wannan hutun don musulmai suyi bikin sallar eid-el-fitr

Ministan aikace-aikacen cikin gida  Lt.-Gen. Abdulrahman Dambazau (Rtd.) yayi wannan sanarwa ranar alhamis 22 ga watan Yuni a garin Abuja.

Dambazau ya yi gargadi akan yan kasar su daina yaɗa kalamin tunzura,ya kara da cewa ko wani dan kasa yana da hakkin zama a duk inda ya gan dama.

Ministan yace gwamnatin tarayya na da ikon tura dakarun jami’in tsaro inda ta gan ana neman haifar da rikici.

Advertisement

Ministan yayi kira ga musulmai su amfanin da wannan damar ta ranar eid-el-fitr su yi ma kasar addu’ar zaman lafiya da haddin kai

Advertisement
Latest Videos
Advertisement