Sanata ya nemi taimakon sauran sanatoci kan maganar kiranye
A zaman da yan majalisar suka yi ranar talata 4 ga watan Yuli, sanata Dino Melaye ya nemi taimakon sauran sanatoci kan kiranye da mazabar shi ke neman yi.
A rahoton da jaridar premium times ta fitar, sanatan mai wakiltan jihar kogi yayi la’akari da umurni na 14 na dokar majalisar don neman taimakon sauran sanatoci kan batun kiranye da ake neman yi mai.
Yayin da yake jawabi, sanata Melaye ya kara bayyana cewa Gwamna Yahaya Bello ke goyon bayan kiranye da ake neman yi mai.
Wannan neman taimakon ya biyo bayan hukumar zabe na kasar ta fitar da jadawali mai matakai wanda zata bi domin yi wa sanatan kiranye.
Yayi bada amsar neman taimakon, mataimakin shugaban majalisar Ike Ekweremadu ya tabbatar ma sanatan cewa sauran sanatoci na bayan shi dari-bisa-dari har ma ya kara da cewa maganar kiranyen baza ta kai ko ina ba.
Mutum 158,888 daga mazabar sanatan suka sa hannu don tabatar da shirin kiranye ma hukumar zabe.