Advertisement

Tsohon sakataren watsa labarai na marigayi Abacha ya rasu a garin Jos

David Attah
David Attah
Ya rasu a safiyar talata 4 ga watan Yuli a wata asibiti mai zaman kanshi dake Jos, jihar filato
Advertisement

Tsohon kakakin shugaban kasa marigayi  janar Sani Abacha ya rasu yana da shekaru 72 a duniya.

Advertisement

Jaridar premium times ta ruwaito cewa dansa Emmanuel Attah ya sanar cewa ya rasu a wani asibiti mai zaman kanshi a garin Jos a jihar filato ranar talata 4 ga watan Yuli 2017.

Tsohon ƙwamishnan labarai na jihar Benue ya sha fama da rashin lafiya kafin rasuwar sa.

Kafin kasancewar shi kakakin Abacha, Attah wanda ya kammala karatun sa a jami’ar Ahmadu Bello (ABU) ya rike mukamin manaja mai kula da harkoki a ma’aikatar buga takardu na Benue Plateau Publishing Corporation (wanda ake kiran Nigerian Standard ayanzu).

Kuma yana cikin jagororin jaridar Daily Times dake legas.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement