Advertisement

Ministan Buhari, Kayode Fayemi ya ajiye aiki

Tsohon ministan ya mika takardar murabus ga shugaban kasa mako daya da ya shude sai yanzu yin haka zata fara aiki.
Advertisement

Tsohon gwamna yayi hakan ne domin mayar da hankali ga zaben gwamnan jihar Ekiti wanda ya fito takara.

Advertisement

Yace akwai aiki sosai da zasuyi sannan kuma shi da sauran masu takara na kalon wannan zabe mai zuwa a matsayin hanyar ceton al'ummar jihar.

Fayemi yayi gwamnan jihar Ekiti tsakanin 2010 zuwa 2014, bai samu damar zarcewa a wa'adi na biyu da ya nema. Ya fadi ga Ayodele Fayose a zaben jihar da aka gudanar a cikin 2014.

Za'a gudanar da zaben jihar Ekiti a ranar 14 ga watan Yuli 2019.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement