Akalla
Wannan matakin nasu ya biyo bayan wanda takwarorinsu na majalisar dattawa suka dauka na sauya sheka daga jam'iya mai ci.
Sanatoci sha biyar suka yi balaguro daga jam'iyar APC zuwa PDP cikin su har da sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Mutum daya cikin su ya koma jam'iyar ADC.
Makamancin haka ya faru a farfajiyar majalisar wakilai bayan wasikar da kakakinta Yakubu Dogara ya karanta bayan yan majalisar sun sa hannu.
Mutum 32 daga cikin su sun koma jam'iyar PDP yayin da 4 kuma suka koma ADC sabon jam'iya da tafiyar Coalition for Nigeria Movement wanda cif Olusegun Obasanjo ya kirkiro.
Har ila yau dai daya daga cikin su bai bayyana jam'iyar da zai koma.
Yan majalisar sun ce rabuwar kawunan yan'yan APC yayi sanadin daukar matakin barin ta.
Ga sunayen wadanda suka koma jam'iyar PDP kamar haka;
Garba Umar (Kano)
Olayonu Tope(Kwara
Ahmed Garba (Kano)
Kabiru Marafa (Sokoto)
Zakari Mohammed (Kwara)
Abubakar Amuda-Kanike (Kwara)
Ali Madaki (Kano)
Hassan Saleh (Benue)
Ahman Pategi (Kwara)
Mark Gbillah (Benue)
Shehu Usman (Kano)
Aminu Shagari (Sokoto)
Nuhu Danburam (Kano)
Atunwa Abdulrazak (Kwara).
Salisu Zakari (Bauchi)
Hassan Omale (Kogi)
Rufai Chanchangi (Kaduna)
Abdulsamad Dasuki (Sokoto)
Sani Zoro (Jigawa)
Benjamin Okolo (Kogi)
Funke Adedoyi(Kwara)
Bode Ayorinde (Ondo)
Bashiru Salihu (Sokoto)
Barry Mpigi (Rivers)
Nasiru Sule (Kano)
Segun Ogunwuyi (Oyo)
Lawal Rabiu(Kaduna)
Sani Rano (Kano)
Dickson Tarkighir (Benue)
Musa Adotsamiya (Kano)
Emmanuel Udende (Benue).
Mutune hudu daga cikin yan majalisar da suka koma jam'iyar ADC sun hada da Sunday Adepoju (Oyo), Olugbemi Samson (Oyo), Taiwo Michael (Oyo) and Olasupo Abiodun (Oyo).
Emmanuel Orker-Jev daga jihar Benuewanda shine na karshe da ya fice daga APC bai bayyana sabon jam'iya da zai koma.