Advertisement

Shugaban majalisar dattawa ya yaba kokarin da kannywood keyi

Bukola Saraki ya kuma jinjina masu bisa gudummawar da suke bada wa na samad da aikin yi ga matasa a masana'antar.
Advertisement

Shugaban bayyana hakan ne bayan ya amshi bakoncin jaruman shirin "Mutum da addininsa" karkashin jagorancin Salisu Aliyu 'chal'.

Advertisement

Saraki yace yan wasan kannywood suna taka rawar gani wajen nishadantar da al'umma cikin yaren hausa.

Ya kuma jinjina masu bisa gudummawar da suke bada wa na samad da aikin yi ga matasa a masana'antar.

Salisu Aliyu wanda ya shirya fim din "Mutum da addininsa"ya jagorancin sauran jaruman shirin da suka hada da Ali Nuhu da Tijjani Faraga da Maryam Habila zuwa wajen Saraki.

Jaruman sun kai ma shugaban majalisar dattawa ziyarar ta musamman a ofishin sa dake Abuja.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement