Advertisement

Ƙungiyar matasa sun ƙalubalanci shugaban kasa da ya yi murabus cikin maƙonni 8

Nigerian President Muhammadu Buhari has been on medical leave in London since the beginning of May
Nigerian President Muhammadu Buhari has been on medical leave in London since the beginning of May
ƙungiyar tace matasa miliyan bakwai zasu tsige shi daga mukamin shi idan bai yi murabus
Advertisement

Wata ƙungiyar matasa mai suna ‘matasan nijeriya masu neman adalci’ watau “Nigerian Youth Advocate for Justice” sun ƙalubalanci shugaba Muhammadu Buhari  da yayi murabus kasancewar barin kasar da ya yi har kwana 53.

Advertisement

Ƙungiyar ta ba shugaba makonni 8 da ya yi murabus ko kuma matasa miliyan 7 daga jihohi 22 zasu tsige daga mukammin shi.

Shugaban ƙungiyar, Seriki Olorunwa yace, rashin lafiyar shugaban kasa yasa ba zai iya cigaba  da mulkin kasar.

“Muna kira ga majalisar dattawa, majalisar wakilai, majalisun jihohi da sauran su da su yunkura wajen ganin cewa shugaba ya yi murabus don amfanin yan kasa.’ Olorunwa yace.

Ya kara da cewa matasa a shirye suke wajen cimma buri su har ma ya bada tabbaci cewa wannan zai faru ba tare da zubar da jini.

Advertisement

Dangane ga kashe-kashe, garkuwa da mutum da kuma sace-sace dake yaduwa a kasar, ƙungiyar tace jam’iyar APC ta wulakanta yan nijeriya don son kai.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement